"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Thursday, July 17, 2025

END OF TENURE AS PROVOST JICORAS BABURA

HADEJIA A YAU!


On Tuesday, 15th July 2021, the then Jigawa State Governor appointed me as Provost of Jigawa College of Remedial Advanced Studies, Babura, for a first term of 4 years, renewable for a maximum of 8 years as enshrined in the college's law.

 Alhamdulillah, I announce my departure and handing over of my position as PROVOST with the successful 5 year Accreditation of the 10 ND Programs I introduced in the college after been appointed as provost, and a Historic First Certification Exams ever conducted in Jigawa State for 2 National Diploma on Health Science Courses (ND Public Health Technology and ND Epidemiology & Desease Control Technology) with over 120 external candidates from within and outside Jigawa State. This marks the end of my First Tenure of four (4) years as the Pioneer Provost of the College.


My special prayers and appreciation go to His Excellency Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, Mni, MON, the Former Governor of Jigawa State and Minister of Defence of the Federal Republic of Nigeria, who found me worthy and appointed me to head this wonderful institution. This is after several attempts to include me in his government.

A special thanks go to my Leaders in struggle, the Former and the Present Chairmen of our great association, “HADEJIA INA MAFITA INITIATIVE”, in persons of DR ISAH BILLAMI and SIR. Dr Baidi Mohammed Gajo Yalleman and the entire Mafita family, who not only supported me but also made this wonderful journey a success and a reality. 


I also thank the pioneer Chairman and members of JICORAS Governing Council, Professor H.I. Bayero. And the present Governing Council of Hajiya Gaji Bello Hussain for their support, cooperation and giant efforts to uplift JICORAS in achieving academic excellence.

My Colleagues, the Management and other teaching staff of JICORAS, especially my former Registrar, Dr Rabiu Sale Kazaure, and the present Acting Registrar, and the entire management.  My appreciation also goes to my Deputy and Ag. Provost whom I handed over the affairs of the college to in person of Malam Bashir Ubale Gumel, who is always with me in every decision (soft or hard) I took in ensuring high academic standards and quality assurance in the system. 
I pray and hope that the person who will succeed me will do better than I to uplift the image and academic standard of the college.   I learned a lot, heard a lot, and saw a lot during these short but important and memorable four years in office as provost of this institution.

I thank the entire Babura Community and the CBO, Movement for Better Babura, who always supported me with positive advice as a community-based organization.

I always believed in the saying of the Premier of the Defunct Northern Region, Sir Ahmadu Bello, Sardauna, on the civil service
BA A IYAWA!
BAA GAMAWA!!
BASU YABAWA!!!
Dr. Hussaini Shehu
Former Provost JICORAS, Babura and Vice Chairman, Hadejia Ina Mafita Initiative

Wednesday, June 4, 2025

A FADAWA HADEJIYAWA KASUWA. TARIHIN KAFUWAR GANDUN BUNDUGOMA

HADEJIA A YAU!
TARIHIN KAFUWAR GANDUN BUNDUGOMA. 

Daga Umar Yusuf Da'awa 

A Zamanin Mulkin Sarkin Haɗejiya Haru Bubba wadda ya yi mulki a shekarar 1865-1885 ne, kasuwa ta mamaye Kudancin Haɗejiya, Ma'ana ɓagaren Kudu da garin Haɗejiya. Kasuwa ta kafu jama'a sun shigo garin Haɗejiya, kama daga Turawa (Turkiyya) Larabawa dama Hausawammu na gida da na wajen kasar nan. 

Saboda shahara da Haɗejiya tayi na noman Gyaɗa da Auduga da Dawa da Gero dadai sauran su, wannan tasa jama'a suka shigo Haɗejiya daban daban. Haka aka yi ta kasuwanci a wannan yanki, har akwai lokacin da Jirgi yakan sauka a Haɗejiya mai sauƙar Ungulu na larabawa da Turawa a basu Auduga da gyaɗa, su kuma su kawo mana tufafin irin su Abaya da kayan mulki irin na gabas. Kasuwa tayi ƙarfi jama'a sun cika, sai ɓarayi suka fara ziyartar wannan kasuwa suna yin wasoso, har labari ya iskewa Sarki, nan take sarki ya tashi ɗaya daga cikin Fadawansa a bangaren 'Yan Baka wadda ake ƙira da Bundugoma, yace yaje ya sa ido ga yan kasuwa ya tabbatar sun yi saye da sayarwa lafiya babu tsoro. 

Bundugoma ya amsa umarnin sarki, in ya tafi tun Safe har yamma shi da yaran sa suna kula da 'yan kasuwa. Da yaga haka kawai sai ya tare wannan wuri gaba ɗaya da zama, ya share fili ya gina bukkar sa tare da yaran sa. Wannan tasa har yau ake ƙiran wannan wuri da Gandun Bundugoma. Bundugoma kuwa ana nufin mai Bindiga a yaren Manganci, domin shi Bamange ne. Kuma sune suke Sarautar Galadiman Bindiga a Hadejia. Kasuwa ta ci gaba da ci, kuma tafi cika ranar Lahadi saboda Baki suna zuwa ne ranar Asabat su kwana lahdi su ci kasuwa su wuce. 

A zamanin sarkin Hadejia Abdulkadir Turawa suka umarci a dawo da kasuwa yamma da gari don dacewa da zamani, sai kasuwa ta dawo duriyar yamma da gari wato Unguwar Rinde inda kasuwa take yanzu.